Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo, ta nuna damuwa game da shirin wasu kasashen Turai guda biyar na tisa keyar ‘yan gudun hijira zuwa Rwanda.
Kinshasa ta kuma nuna damuwa kan sakamakon da ya haifar da rikicin gabashin DRC, kafin ta yi Allah wadai da shi a cikin wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Waje.
“Muna Allah wadai da wannan kawancen da aka tsara da Rwanda kuma muna kira ga abokan huldarmu na Turai da su nuna daidaito a cikin alkawuran da suka yi na kasa da kasa,” in ji Ministan Harkokin Wajen Congo Thérèse Kayikwamba Wagner a cikin wata sanarwa.
Kasashen biyar na Tarayyar Turai da suka hada da Jamus, Austria, Denmark, Girka, da Netherlands sun sanar a ranar 16 ga Nuwamba shirinsu na mayar da ‘yan gudun hijira marasa takardu ko wadanda aka ki amincewa da neman mafakarsu ko aka koresu zuwa kasarsu ta asali zuwa Rwanda.
Wannan shawarar ta haifar da rashin gamsuwa a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo (DRC), wadanda suka nuna adawa da ita.
Duk da cewa gwamnatin DRC ta amince da ‘yancin abokan huldarta na ayyana manufofin kaura, duk da haka ta aza ayar tambaya game da alƙawarin da aka yi wa dokokin ƙasa da ƙasa.