Search
Close this search box.

Biden : Netanyahu “Yana Cutar Da Isra’ila Ta Hanyar Yakin Gaza

Shugaba Joe Biden na Amurka ya bayyana cewa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu “yana cutar da Isra’ila fiye da samar mata alheri” ta hanyar yakin da

Shugaba Joe Biden na Amurka ya bayyana cewa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu “yana cutar da Isra’ila fiye da samar mata alheri” ta hanyar yakin da ya ke a Gaza.

“Yana da ‘yancin kare Isra’ila, ‘yancin ci gaba da kai hari kan Hamas, Amma dole ne, dole ne ya mai da hankali kan rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, ” in ji shugaban na Amurka a wata hira da tashar ta MSNBC.

A baya baya nan dai gwamnatin Amurka ta fara sukan yakin da Isra’ila ke jagoranta kan Gaza, inda masana da dama ke ganin hakan bai rasa nasaba da sukan da gwamnatin ke sha a daidai lokacin da zaben Amurka ke karatowa.

Ko a kwanan baya ma mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Haris ta bukaci ISra’ial ta kawo karshen yakin nan take.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments