Search
Close this search box.

Babban Taron China Da Afirka Na Ci Gaba Da Gudana A Birnin Beijin

Shugabannin kasashen Afirka da na China suna ci gaba da gudanar da zaman taronsu a birnin Beijin, wanda yake yin dubi kan muhimamn batutuwa da

Shugabannin kasashen Afirka da na China suna ci gaba da gudanar da zaman taronsu a birnin Beijin, wanda yake yin dubi kan muhimamn batutuwa da suka shafi kara karfafa alaka tsakaninsu.

A nasa bangaren shugaban kasar ta China Xi Jinping ya yi alƙawarin ba da tallafin kuɗi na sama da dala biliyan 50 ga ƙasashen Afirka a tsawon shekaru uku masu zuwa, tare da taimakawa wajen samar da ayyukan yi kusan miliyan daya a nahiyar.

”A cikin shekaru uku masu zuwa, gwamnatin China tana son ba da tallafi na kuɗi na Yuan biliyan 360, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 50.7,” kamar yadda Shugaba Xi ya shaida wa shugabannin Afirka a ranar Alhamis a birnin Beijing, inda ya kuma yi alƙawarin samar da ayyukan yi aƙalla miliyan ɗaya ga ‘yan Afirka.

Kusan shugabannin ƙasashen Afrika 50 ne tare da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres suka halarci babban taron China da Afrika a wannan mako, kamar dai yadda kafar yada labarai ta kasar ta bayyana.

Tuni dai har shugabannin na Afirka suka samu gagarumin alƙawarin zurfafa haɗin gwiwa a fannonin ababen more rayuwa da noma da haƙar ma’adinai da kusuwanci da kuma makamashi.

Da yake jawabi ga shugabannin a yayin buɗe taron a birnin Beijing, Shugaba Xi ya yaba da dangantakar da ke tsakanin China da nahiyar a matsayin “lokaci mafi kyau a tarihi”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments