Ana Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Imam Ali (A.S)

Yau Talata daruruwan miliyoyin musulmi mabiya mazhabar shi’a na gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar Imam Ali (AS), limamin shi’a na farko. Ranar dai a

Yau Talata daruruwan miliyoyin musulmi mabiya mazhabar shi’a na gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar Imam Ali (AS), limamin shi’a na farko.

Ranar dai a Iran wace hutu ce ga kowa ana mata lakabi da ‘’ranar Uba’’, inda a yayinta ake aikewa da sakonnin yabo da ziyarce-ziyarce da kyautuka ga mahaifi.

An haifi Ali bn Abi Talib (AS) shekaru 23 kafin Hijira, manzon tsira Annabi Muhammad (SAW) daga birnin Makka zuwa Madina.

Imam Ali mutum mai kima da daraja a tsakanin musulmi, Shi ne mijin diyar Manzon Allah, Sayyada Fatima Zahra, kuma mahaifin Imam Hassan da Hussaini (AS) da Sayyida Zainab da Ummu Kulthum.

Yana da babban matsayi a tsakanin musulmi saboda jarumtakarsa, da tsayin daka kan kiyaye adalci da daidaito.

Surukin Annabi Muhammad, Imam Ali, ya yi shahada ne bayan da Ibn Muljam ya sare shi da takobi mai guba, a lokacin da yake gabatar da sallarsa a babban masallacin Kufa, wanda yake a kasar Iraki a yanzu, kuma ya yi shahada a ranar 19 ga watan Ramadan bayan kwana biyu na jinya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments