Da yammacin asabar ne Senegal ta karbi bakunci gasar Olympics na matasa ta bazara ta shekara ta 2026. kuma Wannan ne karon farko da ake gudanar da gasar a nahiyar Afirka.
Tuni dai wutar gasar ta isa birnin Dakar bayan ta zagaya sassan kasar a matsayin wata alama da ke nuna shirye shiryen sun kankama.
An kaddamar da bikin a hukumance a babban filin wasa na Abdoulaye Wade da ke birnin Diamniadio mai tazarar kilomita daga Dakar da misalin ƙarfe 6 agogon kasar.
Matasan ƴan wasa kimanin 2700 daga kasashe 206 a fadin duniya za su fafata a wasanni 25 da za’a yi tsawon makonni biyu. A karshen gasar ana saran rarraba lambobin yabo da kyaututtuka 153 ga wadanda su kayi nasara.