Falasdinawa Biyu Sun Yi Shahada A Harin Da Isra’ila Ta Kai Gaza

Wasu Falasdinawa biyu sun yi shahada a wani hari da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a Gaza, kuma gobara ta kashe jarirai biyu a Khan

Wasu Falasdinawa biyu sun yi shahada a wani hari da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a Gaza, kuma gobara ta kashe jarirai biyu a Khan Younis

Wani Balasdine ya yi shahada a safiyar yau Asabar sakamakon harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar zirin Gaza, yayin da wani mutum ya yi shahada sakamakon raunukan da ya samu a wani hari da aka kai a baya a birnin Gaza. A halin yanzu kuma, gobara da ta tashi a wani tanti da ke dauke da mutanen da suka rasa matsugunansu a yankin Mawasi na Khan Younis gobarar ta yi sanadiyyar mutuwar ‘yan mata biyu.

WaÉ—annan abubuwan suna daga cikin keta yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, wadda ta fara aiki tun daga watan Oktoban shekara ta 2015.

Wata majiya daga asibiti mai zaman kansa na Al-Awda da ke tsakiyar yankin Gaza ta ruwaito mutuwar Bafalasdine Diaa Abu Al-Rous sakamakon harin sama da Isra’ila ta kai arewacin sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted