Ana Ci Gaba Da Zanga-zangar Yaki Da Tsadar Rayuwa A Faransa

ana ci gaba da yaki da zanga-zangar yaki da tsadar rayuwa a kasar faransa da kuma neman macron ya yi murabus

Rahotanni sun bayyana cewa ana ci gaba da zanga zanga a wasu birane a kasar faransa inda dalibai da kungiyoyin ma’aikata da masu nuna goyon bayansu ga kungiyar yello vest , da kuma nuna adawa da tabarbarewa yanayin rayuwa da ayyukan gwamnati da kuma jaddada  bukatar shugaban kasar Emmanuel marcron ya yi murabus, tare da yin kira da a rufe cibiyoyin ilimi daga ranar talata mai zuwa

Rahotanni da kafafen tada labarai suka wallafa ya nuna cewa gwamantin kasar faransa ta aike da jami’anyan sanda sama da dubu 70 akan tituna da kayan aiki domin shawo kan zanga-zangar a manyan biranen kasar  ganin yadda zanga-zangar take kara ci gaba .

Ana sa bangaren kakakin kungiyar dalibai  sabirin kharbash yayi kira da a rufe makarantun  sakandire da jamioi daga ranar talata mai zuwa inda ya bukaci dukkan daliban da su halarci babbar zanga-zangar da za’a yi a ranar Alhamis mai zuwa  da kuma yajin aiki da kungiyar ma’aikata ta bukaci yayanta su yi

Wadannan kiraye -kirayen suna zuwa ne bayan hutun kaka na makwanni biyu da aka yi da ya kasa shawo kan zanga-zangar, duk da cewa gwamnatin faransa ta sanar da wani shiri na mataki –mataki a wannan makon a yunkurin da take yi na dawo da kwanciyar hankali a kan titunan kasar

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted