Rahotanni sun bayyana cewa wani babban dan majalisa a majalisar shawarar musulunci ta kasar iran yayi gargadin cewa iran za ta mayar da martani mafi muni kan duk wata barazana ba tare da iyaka ba, kuma za ta kai hari ta ko ina, kana ya jaddda cewa Tehran ce kadai za ta tantance lokacin da za’a kawo karshen yaki idan amurka da isra’ila suka sake kai mata hari
Ibrahim Azizi shugaban kwamtin tsaro na majalisa da kuma tsare-tsaren kasashen waje yayi wannan bayani ne a shafinsa na X da yake bayani game da rashin yin sulhu a umarnin da jagoran juyin musulunci na kasar ya bayar ba, yace dokokin iran a fili suke kuma babu wata yarjejeniya a kansu, duk wata barazana to zata fuskanci mayar da martani nan take kuma mafi muni, kuma mara iyaka.
Wannan gargadin yana zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rashin zaman lafiya a mashigar Hormuz inda dakarun sojin ruwa na kasar iran suke ci gaba da iko da shiga da fice tun bayan da amurka da isra’ila suka kaddamar da hari akanta a ranar 28 ga watan fabareru, inda gwamnatin iran ta bayyaance cewa babu wani jirgin ruwa da zai wuce sai ya bi dokoki da sharuddan da iran ta gindaya kuma ya nemi izinin wucewa idan kuma ya ki zai fuskanci mummunan sakamako