Al-Adu Da Ci Gaban Addinin Musulunci A Tarihi (24)

24-Asslamau alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na al-adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, wanda ni

24-Asslamau alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na al-adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, wanda ni Tahir Amin nake kawo mako sau guda a ko wane mako. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///…Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci  gaba da magana masana ilmin haske a zamanin daulolin musulunci, inda muka ambaci  Abu Ali Hassan dan Haitham Basri, wanda aka fi saninsa da Ibn Haitham. Mun ce masani ilmi lissafi kuma babban masani ilmi haske ne a musulmi a cikin karni na 4 hijiri kamari.

Mun kuma kara da cewa  Ibn Haitham yana da babban matsayi a ilmin kanikanci da kimiyyar lissafi, An san shi a cikin littattafan Latin ta Tsakiya a matsayin Alhazen.

Sannan munce, wannan halin ya ci gaba har zuwa karni na 7 hijiri kamari, a lokacinda Qutubud-Deen Shirazi, wani masanin ilmin sanin haske, ya sake maida hankali kan wani bangare na ilmin sanin haske wanda ibn Haitham ya fara amma ya sanya masa suna ‘bakan Gizo’ a nan Iran.

Mun ce, irin ci gaban da masana a kasashen yamma suka samu, a wani bangare mai yawansa, ya ginu a kan ayyukan Ibn Haitham ne.

Da wannan dalilin ne a kasashen yamma ake masa lakabi da ‘baban ilmin sanin haske’.

Daga karshe mun yi maganar cewa, bangare mai yawa na ci gaban da kasashen yamma suka samu dangane da ilmin haske ya faru ne saboda ayyukan masana musulmi a bayan.

A cikin shirimmu na yau muna son mu fahintar da masu saurari irin ci gaban da musulmi a tarihi suka samar a fannin ilmin likitanci da kuma jinya da magunguna, da fatan zaku kasance tare da mu.

Ilmin likitanci, kamar sauran ilmomin da muka yi magana a kansu a cikin shirye shiryemmu da suka gabata, shi ma yana da matukar muhimmanci, kuma masana musulmi sun taka muhimmiyar rawa a bunkasa shi.

A cikin wata ruwaya daga daya daga cikin limamai masu tsarki daga manzon All..(s) yana cewa, a ma’anarsa:{ilmi kashi biyu ne, ilmin jikunkuna da ilmin addin.} .

Wannan hadisin yana nuna matsayi da muhimmancin ilmin likitanci a addinin musulunci ko a cikin musulmi. Sai dai  muna iya tabbatar da cewa, ilmin likitanci, ya shigo hannun musulmi ne ta hanyar tarjama littafai girka ne, musamman  ko kuma littafan  Hippocrates da Galen.

Sai dai da dama daga cikin cututtukan da musulmi suka himmatu da samun magungunansu a lokacin, cututtuka ne wadanda suka shafi kasashensu, a kuma yanayin da wadanda kasashe suke ciki. Da dama daga cikinsu basu zo cikin littafan kasar girka wadanda aka tarjama ba.

A matsayin misali, Zakariyya Razi a cikin littafinsa mai muhimmanci mai suna ‘Kitabul Hawi’, ya gabatar da tsirrai masu maganin fiye da 700 , tare da ambaton amfanin ko wanne daga cikinsu, a magance cututtuka, tsirrai wadanda ba su zo cikin littafan likitanci na masana ilmin likitanci na girka da aka tarjama ba.

Al-hali, a cikin Hippocrates , masanin ilmin likitanci na kasar Girka a bangare tsirrai da magungunansu, bai kawo  wannan adadin ba, ya kawo tsirrai 500 kacal.  

Littafin Hawi na zakariya Razi, shi ne littafi na farko, idan ana maganar ilmin likitanci a lokacin. Masanin ya kawo bayanin cututtuka da dama, ya kuma rarrabesu dalla dalla.

Cututtukan da Razi ya kawo a cikin hawi, tare da bayanin magungunansu daban daban, sun dara na wadanda suke cikin littafin likitanci na ‘Hippocrates’ ko na Galen. Ilmin likitanci a zamanin daulolin musulunci ya soma ne da tarjamar littafan likitanci daga kasar Girka da kuma India a lokacin. Sai kuma a cikin karni na biyu miladiyya, wato kafin bayyanar addinin musulunci da kimani karnuka 4, gwamnatin Romawa ta lokacin ta kori Nestoriyawa wadanda aka sansu da ilmin likitanci daga kasar. Daga nan sai Nastoriyawa suka dawo kasar Farisa na lokacin suka kuma kafa cibiyar ayyukan likitanci, ko mu ce asbiti a garin Jundi-Shapoor.

A nan Jundi-Shapoor ne suka kafa Jami’ar koyon aikin likitanci, na kasar Garka da kuma na kasar India wanda suka tarar a wurin.

Bayan shigowar addinin musulunci kasar Farisa, wannan cibiyar aikin likitanci ya taka rawar a zo a gani, wannan samar da likitoci musulmi, da kuma ci gaba ilmin likitanci a cikin al-ummar musulmi.

A gaskiya, daya daga cikin cibiyoyin ilmin likitanci da suka taimaka wajen kawo ci gaba a ilmin likitanci a cikin daulolin musulunci ita ce Jundi-Shapoor.

Jundi -Shapoor Jami’a ce kuma asbiti ne mai muhimmanci wanda yake kuma taimakawa wajen tarjamar littafan likitanci, daga harsuna girka da farisanci da kuma Siryananci. Asbitin Jindi- Shapoor shi ne mafi tsufan asbitoci a daulolin musuluci wanda aka gina shi tun zamanin sarki Shapoor na II daga sarakunan farisawa kafin musulunci.

Wannan asbitin, tare da taimakon likitoci da malamansu, ya dauki karnuka uku yana aiki wajen yada ilmin likitanci a tsakanin al-ummar musulmi ya kuma taimaka wajen wayewarsu.

A cikin wannan cibiyar ilmin likitanci ne, aka samar da yayan wani gida,  likitoci da masana ilmin kiwon lafiya har 12 na tsawon karnuka. Banda haka sun zama likitocin sarakunan da dama daga cikin sarakunan Abbasiyawa. Kuma sune yan gidan Bakhteshoo.

Yayan wannan gidan sun fara ayyukan likitanci tun rabin karni na biyu hijira kamariyya, har zuwa tsakiyar karni na biyar kamariyya. Sun zama likitocin sarakuna, ko masu bada shawara garesu ko kuma sun tarjama littafai daga wasu harsuna zuwa harshen larabci.

Sannan  yan gidan Barmaki a zamanin sarakunan Abbasiyawa, musamman sarki Harunar Rasheed, sun gina asbiti babba a Bagdaza suka mikawa wani likita dan kasar Indiya mai suna Ibn Dahin asbitin ya kula da shi, sannan ya tarjama ilmin likitanci na Sanskrit. Daga baya wannan asibin ya zama, misali ga sauran yankuna a kasashen musulmi, wanda yasa suka gina irinsa a yankunansu.

A farko farkon khalifancin Abbasiyawa ne, hankalin sarakuna ya koma kan ilmin likitanci na girka da kuma Roma ta gabas. A shekara ta 148 ne sarki mansur dawaniki sarki na biyu daga cikin sarakunan Abbasiyawa, saboda rashin rafiyar da ta same shi, ya gayyaci likitoci yan gidan Bakhtishoo daga Jundi-Shapoor zuwa Bagdaza suka kuma sami nasarar jinya da kuma warkar da shi. Daga nan mansur ya fara himmatuwa da yan gidan, haka ma sarukanan da suka zo bayansa. Daga nan likitoci yan gidan Bakhtishoo suka dawo Bagdaza, suka kuma shahara a ayyukan likitanci da jinya.

A dai dai lokacinda lokacinda ayyukan tarjamar littafan girma ya kai koli, sai ra’ayin likitanci na girma ya zama shi ne ya mamaye ko ina a cikin daular musulunci a lokacin. Littafin ilmin likitanci da jinya mafi muhimmancin da aka tarjama zuwa harshen larabci a lokacin shi ne ‘Dioscorides’, wanda yake magana dangane da daddaikun kalmomin da suka shafi ilmin likitanci.

A farkon karni na 3 hijira kamariyya, bayan an kama mu’assasar darul Hikima, masana da dama suka fara tarjamar littafan likitanci daga kasashen waje zuwa harshen larabci.

Fitacce, kuma mutumin da yafi kowa yawan tarjama a darul Hikima a lokacin shi ne Ishak Abbadi. Hunain dan Aglab, da dansa Ishak, sukan tarjama littafan likitanci zuwa larabci. Kuma bayan Mutuwar Hunain, an tabbatar da cewa ya tarjama littafan Galen har guda 95 zuwa harshen larabaci sannan wasu 34 zuwa yaren siryananci.

Banda haka Hunain, bayan aikin tarjama, yana wallafe wallafen littafan likitanci. Daga cikin littafan da ya wallafa akwai littafi mai suna ‘Masa’il fi ilmil Tiibi lil muta allimin’.

Dangane da ilin cututtukan ido kadai Hunain ya wallafa littafi mai suna ‘Ashara Makalat fil Aini’. da haka kuma Hunain da sauran masu tarjama, ta hanyar ayyukan tarjama da kuma wallafe wallafe sun gabatar da gudumawa mai yawa a fagen ilmin likitanci a cikin al-ummar Musulmi.

Fitaccen likita daga Nestoriyawa wanda ya ke aikin likitanci a jami’ar likitanci ta Jundi-Shapoor shi ne Abu Yahanna Masuyyeh, wanda aka fi saninsa da dan Masuyyeh.

Ibn Masuyyeh kaɗai yana da rubuce-rubuce masu ban mamaki a cikin Larabci game da matsalolin kiwon lafiya da suka shafi nau’i zazzabi daban-daban, kuturta, baƙin ciki, cututtukan ido, da matsalolin abinci mai gina jiki.

Wani sanannen masanin ilmin likitanci shi ne Abul Husayn Ali ibn Sahl Rabban Attabari.

Tabari, a cikin littafinsa  mai suna ‘Firdaws al-Hikmah’, ya yi bayani game da hanyoyin maganin Girka, da na Romawa da kuma Indiyawa.

Wannan littafin shine cikakken littafin likitanci na farko wanda ya yi tasiri sosai ga likitocin da suka zo daga baya.

Ka’idojin da Tabari ya kawo su a cikin littafin nsa, suna da matuƙar muhimmanci a fannin sanin cututtuka, magungunansu da kuma ilimin magunguna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted