Jami’in Iran: Akwai Bukatar Kara Yawan Yuranium Da Ake Tacewa

Jami’in Iran ya bayyana cewa: Ya kamata a sanya ajandar ƙara yawan sinadarin Uranium da ake tacewa zuwa kashi 90%, kuma a yi Shirin tunkarar

Jami’in Iran ya bayyana cewa: Ya kamata a sanya ajandar ƙara yawan sinadarin Uranium da ake tacewa zuwa kashi 90%, kuma a yi Shirin tunkarar duk wani yanayi da faru

Memba na Kwamitin Tsaron Kasa da Manufofin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci (wato Majalisar Dokokin Iran) Ibrahim Reza’i ya yi kira da a karfafa karfin makamashin nukiliyan Iran da tsaron kasa da kuma sake duba akidar Shirin makamashin nukiliyar kasar.

Kamfanin Dillancin Labaran Mehr ya ruwaito cewa: Ibrahim Reza’i, memba na Kwamitin Tsaron Kasa da Manufofin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci wato Majalisar Dokokin Iran kuma wakilin mutanen Dashtestan, ya jaddada a wata hira da kafar watsa labarai ga hukumar makamashin nukiliyar Iran kare muhimmancin kiyayewa da karfafa karfin makamashin nukiliya da na soja na Iran. Ya yi kira da a yi nazarin zabin tace sinadarin uranium zuwa kashi 90% kuma kada a yi watsi da sinadarin da aka tace da ya kai kashi 60%.

A cikin hirarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr, ya kuma tattauna ci gaban da aka samu a fafatawar da aka yi da Amurka, matakin shirye-shiryen tsaron Iran, makomar tattaunawa, muhimmancin mashigar teku ta Hormuz a cikin daidaiton tsaro da tattalin arziki da kuma rawar da Majalisar Dokoki za ta taka wajen tallafawa sojojin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted