Iran: Har Yanzu Baa Yanke Shawara Ba Kan Manufofin Nukiliya Ba

Babban sakataren majalisar tsaron kasa na kasar iran yace har yanzu baa tantance game da batun nukiliya ba

Mejor Janaral Muhsen Reza’I babban sakataren koli na majalisar tsaron kasa a iran ya bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa kan yiyuwar iran ta ci gaba da rike manufofinta kan makaman nukiliya idan aka sake kaddamar da yaki a kanta, yace kalaman da amurka take yi sun canza baki daya

Babban jami’in yayi wannan bayani ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin din kasa yace mun karbi wasika daga mataimakin shugaban kasar Amurka JD Vance sai dai har yanzu bamu bada amsa a hukumance game da abubuwa da wasikar ta kunsa ba, amma babu wani mataki a hukumance ko na gwamnati da aka dauka game da manufofin iran kan shirin nukiliya

Haka zalika ya kara da cewa sauya yanayin kalaman Amurka ba kuskure ba ne, domin ta canza yanayin kalamanta baki daya wanda wannan wata alama ce mai kyau sosai, yace mun gode ma Allah alummar iran na ci gaba da riko da karfinta da kuma nasarorinta

A tattaunawar da yayi a baya bayan nan da ya hada da wanda yayi da gidan talabijin din Aljazeera a watan Satumba babban jami’in tsaro ya jaddada matsayin jagoran juyin muslulunci  game da fatawar haramcin mallakar makaman kare dangi , sai dai yayi gargadin cewa ci gaba da kai hare haren amurka da isra’ila da kuma matsin lamba zai iya sanya wa Tehran ta sake nazari kan kasancewarta mamba a yarjejeniyar NPT

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted