Daruruwan yahudawa ne suka gudanar da zanga zanga a kan tituna a birnin tel aviv da wau birane inda suka yi kira ga jam’iyar adawa ta hada kai da bangaren larabawa don kafa gwamnatin da za ta kwo karshen shugabancin fira ministan banejamin natanyaho a isra’ila
Wannan zanga-zangar tana zuwa ne bayan kammala zaben da aka gudanar a ranar talata da ta gabata inda babu wata jam’iya da ta samu kujerun da ake bukata da za ta iya kafa gwamanati daga cikin kujeru 120 na majalisar Knesset
Haka zalika rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da irin wannan zanga zanga a birnin kudus, Haifa da kuma yankunan dake arewaci, inda magoya bayan Natanyaho suka gudanar da zanga zangar adawa a wuri daya, inda wasu daga cikinsu suka rika rere taken nuna wariya tare da zargin jam’iyar larabawa da sace zaben