Mujallar Wall Street journal ta bayyana cewa: Kudaden da Amurka ta kashe a yakin da ta yi da Iran sun kai dala biliyan 47.1
Jaridar Wall Street Journal ta ruwaito cewa: Kudin yakin da Amurka ta kashe kan Iran zai kai dala biliyan 47.1, ban da lalacewar sansanonin sojin kasashen yankin tekun Farisa da aka kiyasta ya kai dala biliyan 5.
Kamfanin dillancin labaran Mehr ya ruwaito cewa: Jaridar Wall Street ta bayyana a cikin wani rahoto cewa: kudin yaki da aka kashe da Iran zai kai dala biliyan 47.1, ban da lalacewar sansanonin soji da aka kiyasta ya kai dala biliyan 5.
Ta kara da cewa harin makami mai linzami na Iran kan sansanin sojin sama na Muwaffaq Salti na Jordan a watan Yulin da ya gabata ya lalata gine-gine kimanin 19 da ke dauke da sojoji.
“Harin kan sansanin ya kasace daya daga cikin mafi munin dare na yakin.”
Binciken ya kara da cewa: Harin Iran ya haifar da mutuwar sojojin Amurka uku a daya daga cikin “dararen da suka fi muni na yakin ga sojojin Amurka.”
Jaridar ta kara da cewa: harin na watan Yuli ya nuna “wani sauyi mai tayar da hankali a dabarun Iran, wanda ya nuna ingantaccen ikon kai hare-hare da kai farmaki kan makiya.”
Rahoton ya bayyana cewa gine-gine 274 a wurare 24 sun nuna alamun lalacewa daga harin Iran a cikin watanni 6 na farko na yakin.