Alummar Yamen Sun Jinjinawa  Iran Game Da Kokarin Da Tayi Na Karya Takunkumin Da Aka Kakaba Musu

Dubban daruruwan alummar kasar Yamen ne suka gudanar da gagarumar zanga-zanga a birnin sa’ada domin nuna goyon bayansu ga kasar iran kan matakin da ta

Dubban daruruwan alummar kasar Yamen ne suka gudanar da gagarumar zanga-zanga a birnin sa’ada domin nuna goyon bayansu ga kasar iran kan matakin da ta dauka wajen ganin ta karya takunkumin da kasar saudiya ta kakaba musu.

Masu zanga-zangar sun nuna gamsuwarsu da kuma jinjinawa alummar kasar iran a matsayinsu na yan uwansu game da matakin dan adamtaka da suka dauka na karya takunkumin da aka sanya musu.

An gudanar da zanga-zangar ne bayan kiran da shugaban kungiyar Asarullah Abdulmalik huthi ya yi bayan da kasar saudiya ta kai sabon hari kan kasar, a lokacin zanga zangar jumaar gargadi da jan hankali, mahalarta taron sun yi kira da a tsananta kai hare-haren ramuwar gayya kan kasar Saudiya .

bayanan da suka fito sun nuna cewa masu zanga-zangar sun siffata kasar saudiya a matsayin kayan aikin Amurka da isra’ila da kuma baritaniya a yankin. kuma sun jaddada goyon bayansu game da matakin da gwamnatin sana’a take dauka na goyon bayan alummar musulmi da suka hada da alummar falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted