Search
Close this search box.

Al’ummar Musulmi A Fadin Duniya Na Gudanar Da Bikin Babbar Sallah

Al’ummar Musulmi a fadin duniya na gudanar da bukukuwan babbar sallah yau Lahadi. A jiya ne dai Mahajjata suka gabatar da tsayuwar Arfa a Saudiyya,

Al’ummar Musulmi a fadin duniya na gudanar da bukukuwan babbar sallah yau Lahadi.

A jiya ne dai Mahajjata suka gabatar da tsayuwar Arfa a Saudiyya, inda yau kuma suke gabatar da Dawafi a dakin Ka’aba.

A Kasashe irinsu, Masar, Lebanon, Jordan, da Turkiyya, Falasdinu, Najeriya da Nijar ma yau ne aka gudanar da bikin babbar sallar.

Al’ummar Gaza sun gudanar da Sallar Idin Al-Adha a cikin baraguzan yankunansu sakamakon lalata gine-ginensu a sakamakon yakin da Isra’ila ta kaddamar kan Falasdinun yau watanni takwas da suka gabata.

A birnin Quds, sojojin Isra’ila sun sake daukar tsauraran matakai kan Falasdinawa da suke kokarin gudanar da bukukuwan Sallar Idi a masallacin Al-Aqsa, tare da hana shiga da kuma cin zarafin masu ibada.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kimanin Falasdinawa dubu 40 ne suka sami damar halartar sallah a cikin masallacin, yayin da wasu kuma ba su da wani zabi illa yin sallar a wajen masallacin saboda hana su shiga.

A nan Iran da kasashe irinsu Malaysia, Iraki, Indiya, da Oman da Senegal sai gobe Litinin za’a gudanar da bikin babbar sallar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments