Search
Close this search box.

Akidar Kin Musulunci Da Musulmi Na Kara Yaduwa A Kasar Burtaniya

Cibiyar ‘Tell Mama’ wacce take kula da al-amuran kin musulmi a kasar Burtaniya ta bayyana cewa yawan halayen kin musulmi a addinin musulunci yana karuwa

Cibiyar ‘Tell Mama’ wacce take kula da al-amuran kin musulmi a kasar Burtaniya ta bayyana cewa yawan halayen kin musulmi a addinin musulunci yana karuwa a kasar Burtaniya.

Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS ya bayyana cewa tashe tashen hankula nan da can, a wasu garuruwa a kasar Burtaniya, wanda wasu kungiyoyi ko matasa masu wuce gona da iri suke haddasawa sun fara yaduwa sun  kuma fara zama barazana ga musulman kasar.

Labarin ya kara da cewa a cikin yan kwanakin da suka gabata irin wadan nan matasa sukan kai hare hare kan masallatai da wuraren ibada  na musulmi, sannan sukan fasa shagunasu su kwace kayaki su kuma kai hare hare kan gidajensu a wasu lokuta.

Gwamnatin kasar Burtaniya ta yanzu, da kuma Jami’an tsaron kasar  suna fama da irin wadannan matsaloli a kasar ta Burtaniya a halin yanzu, inji cibiyar.

Tell Mama ta kara da cewa an  kai hare hare kan akalla masallatai 10 ko kuma an yi barazanar kai masu hare hare, a garuruwan Southportda Hartlepool da kuma Leverpool.  Mata masu hijabi suna cikin tsaro a duk lokacinda suka shiga cikin gari.

Wannan yana faruwa ne bayan da wani matsahi dan shekara 17 a duniya ya  kai hari kan azuzuwan makarantun rani da ake gudanarwa a wasu yankuna a kasar, tare da amfani da wuka. Duk da cewa jami’an tsaron kasar sun bayyana cewa Axel Rudakubana ne suke tuhuma da kai harin, amma wasu mutane a kasar suna dorawa musulmi alhakin kai hare haren.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments