Babu matsin lambar da zai hana Iran hakkinta na nukiliya_Baghaei

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa babu wani nau’in matsin lamba da zai hana Iran hakkinta na amfani da makamashin nukiliya. Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen, Iran ne ya bayyna hakan a wannan Asabar. Esmaeil Baghaei, ya ce “Hakkin Iran na amfani da makamashin nukiliya cikin lumana hakki ne da ba za […]

China za ta dage harajin kwastam ga kasashen Afirka

Kasar China za ta dage harajin kwastam ga kusan dukkan kasashen Afirka, in ban da Eswatini, daga ranar 1 ga Mayu 2026, in ji shugaban kasar Xi Jinping. Mista Xi, ya bayyana cewa matakin zai ba da damar samar da sabbin damammaki ga ci gaban Afirka. Tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanya […]

Iran ta bukaci tarayyar turai ta sauya halayenta game da Tehran

Iran ta bukaci kungiyar tarayyar turai da ta sauya halayenta marasa kyau game da Tehran. Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ce dole ne Tarayyar Turai ta sake duba halayenta “marasa inganci” ga Tehran. Araghchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Cyprus, Constantinos Kombos, wanda kasarsa ke […]

Tarayyar Afirka ta bukaci a dakatar da kisan gilla a Falasdinu

Tarayyar Afrika ta bukaci da a dakatar da kisan gilla da ake wa al’ummar Falasdinu. Sabon shugaban kwamitin kungiyar ne, Mahamoud Ali Youssouf ne, ya mika wannan kiran a lokacin bude taron shekara-shekara na kungiyar ta AU karo na 39. Yau Asabar ne aka bude taron kungiyar a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha wanda […]

MDD ta yi Allah wadai da Isra’ila kan hana kai agajin jin kai Gaza

Majalisar Dinkin Duniya (MDD), ta yi Allah waidai da Isra’ila kan hana shigar da kungiyoyin agaji a zirin Gaza. Mai magana da yawun Majalisar Stéphane Dujarric, wanda ya ambaci Ofishin Kula da Harkokin Jin Kai na (OCHA), ya nuna cewa kungiyoyin MDD na kokarin daidaita ayyukan jin kai saidai hukumomin Isra’ila sun hana kungiyoyin da […]

Ali Shamkhani: Babu Tattaunawa Akan Makaman Iran Masu Linzami

Sakataren Majalisar Tsaron Iran Admiral Ali Shamkhani ya ce; “Makamai Masu Linzami da muke da su, suna cikin jan layin da mu ka Shata da babu yadda za a yi tattaunawa akan makoarsu.” Real Admiral Ali Shamkhani ya kara da cewa;makamai masu linzamin da Iran din take da su wani yanki ne na tsarin tsaron […]

Najeriya: Jerin gwano domin nuna cikakken goyon baya ga Jamhuriyar Muslunci ta Iran

A yammacin ranar Juma’a 13 ga watan Febrairu ne musulmi suka gudanar da gagarumin jerin gwano gangami a cikin birnin kano da ke arewacin Najeriya, domin nuna cikakken goyon bayansu ga jamhuriyar Musulunci ta Iran. A yayin jerin gwanon an yi ta rera taken la’antar Amurka da Isra’ila, kamar yadda kuma aka kona mutum-mutumin Donald […]

Iran: Limamin Jumma’a A Tehran Ya Ce Mutanene Suka Dushe Fitinar Yaki A Kasar

limamin juma'a

Limamin daya jagorancin sallar Jumma’a a nan Tehren Hujjatul Islam Sheikh Mohammad Jawad Hajj Ali Akbari ya bayyana cewa mutanen kasar Iran ne suka dushe wutan fitina da kuma yaki a kasar Iran tare da fitowarsu kan tituna suna goyon bayan jagoran juyin juya halin musulunci suna kuma yin allawadai da masu goyon bayan fitinannu […]

Bincike Ya Nuna Cewa HKI Tana Amfani Da Makamai Masu Tsananin Zafi Kirar Amurka A Gaza

Binciken da wasu masana suga gudanar sun nuna cewa sojojin HKI suna amfani da makamai masu tsananin zafi wadanda suke kona gawakin falasdinawa a cikin karamin lokaci hatta gawakinsu ba za’a samu ba. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto wani shiri na musamman wanda tashar talabijin ta Al-Jazeera na Larabci ta watsa, […]

Islami: Ci Gaban Iran A Fagen Nuklia Abin Mamaki Ne

Shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran Mohammad Islami ya bayyana cewa duk tare da matsin lamda da takurawar da kasashen yamma suka yi ta yi a kan Iran don hana ta ci gaba, amma abin mamaki hatta a wajemmu, mu masi aikin a wannan fannin shi ne, an sami ci gaba mai yawa a […]

Mene ne kason Iran wajen samar da kayayyakin ilimin kimiyya a duniya?

Bayanan ƙasa da ƙasa, ciki har da daga manyan ma’ajiyoyin bayanai masu inganci kamar Scopus da Web of Science, sun nuna cewa a cikin shekaru ashirin da suka gabata, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu matsayi mai muhimmanci a fagen kimiyyar duniya. A cewar Pars Today, masu bincike na Iran suna wallafa dubban takardun bincike […]