Najeriya: Jerin gwano domin nuna cikakken goyon baya ga Jamhuriyar Muslunci ta Iran

A yammacin ranar Juma’a 13 ga watan Febrairu ne musulmi suka gudanar da gagarumin jerin gwano gangami a cikin birnin kano da ke arewacin Najeriya,

A yammacin ranar Juma’a 13 ga watan Febrairu ne musulmi suka gudanar da gagarumin jerin gwano gangami a cikin birnin kano da ke arewacin Najeriya, domin nuna cikakken goyon bayansu ga jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A yayin jerin gwanon an yi ta rera taken la’antar Amurka da Isra’ila, kamar yadda kuma aka kona mutum-mutumin Donald Trump da Benjamin Netanyahu a wurin.

Wasu daga cikin mahalarta gangamin sun sheda wa HausaTV cewa; An daga tutocin Najeriya da na Iran a lokaci guda, domin nuna goyon baya ga jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma tsayawa sahu daya tare da ita game da barazanar shelanta yaki a  kanta da gwamnatocin Amurka da Israila ke yi, tare da jaddada  cewa kaddamar da yaki a kan Iran kaddamar da yaki ne a kan dukkanin al’ummar musulmi.

Harkar musulunci a karkashin jagorancin Sheikh Zakzaky ce  reshen jihar Kano ta yi kira domin gudanar da jerin gwanon, wanda ya samu halartar daruruwan musulmi sunna da shi’a, domin tabbatar da hadin kansu wajen kalubalantar duk wata barazana ko shishigi daga makiya a kan jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A wani bangaren kuma, a ranar 11 ga watan Fabrairu ranar tunawa da zagayowar lokacin nasarar juyin juya halin muslunci a Iran, Gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwa, inda ta ce ta kuduri aniyar kara karfafa dangantakar da ke tsakaninta da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba don taya kasar Iran murnar zagayowar ranar juyin juya halin Musulunci, Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce Najeriya na shirin ci gaba da huldar diflomasiyya da hadin gwiwa mai amfani ga dukkan bangarorin biyu.

A cikin sanarwar da ta fitar, ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta bayyana bikin a matsayin wani muhimmin lokaci na tarihi wanda ke nuna jajircewar Iran ga ‘yancin kai da ci gaban kasa.

Manyan jami’ai daga ma’aikatar harkokin wajen Najeriya sun halarci taron cika shekaru 47 da samun nasarar juyin juya halin musulunci da aka gudanar a ofishin jakadancin Iran da ke birnin Abuja fadar mulkin Najeriya, kamar yadda sauran bangarori daban-daban na al’ummar Najeriya sun halarci wannan taro.


Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted