Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa babu wani nau’in matsin lamba da zai hana Iran hakkinta na amfani da makamashin nukiliya.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen, Iran ne ya bayyna hakan a wannan Asabar.
Esmaeil Baghaei, ya ce “Hakkin Iran na amfani da makamashin nukiliya cikin lumana hakki ne da ba za a iya kwacewa ba, kuma babu wani nau’in matsin lamba ko matsayi na siyasa da zai iya kawar da wannan hakki.”
Ya ce yarjejeniyar hana yaduwar makamman nukiliya ta (NPT) ta amince da hakkin dukkan wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar amfani da makamashin nukiliya don ilimi na zaman lafiya.
Baghaei ya ce tun lokacin da Iran ta amince da yarjejeniyar NPT a shekarar 1970, ƙasar ta bi alkawuranta kuma, saboda haka, ta fifiko cin gajiyar haƙƙin da aka tsara a cikin yarjejeniyar.
Iran tana cikin waɗanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar NPT ta farko, inda ta sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar 1 ga Yuli, 1968. Majalisar Dokokin Iran ta amince da yarjejeniyar NPT a watan Fabrairun 1970, kuma yarjejeniyar ta fara aiki ga Iran daga baya.
A karƙashin yarjejeniyar NPT, an amince da Iran a matsayin kasa mara makamin nukiliya kuma ta amince ba za ta kera ko mallakar makaman nukiliya ba.
Amma a cewarsa Isra’ila ta ki amincewa a duba cibiyoyin nukiliyarta ko kuma a sanya hannu kan yarjejeniyar NPT.
An kiyasta cewa gwamnatin tana da manyan makaman nukiliya 200 zuwa 400 a cikin makamanta, wanda hakan ya sa ita kadai ce ke da makaman ba bisa ka’ida ba a Yammacin Asiya.