Limamin daya jagorancin sallar Jumma’a a nan Tehren Hujjatul Islam Sheikh Mohammad Jawad Hajj Ali Akbari ya bayyana cewa mutanen kasar Iran ne suka dushe wutan fitina da kuma yaki a kasar Iran tare da fitowarsu kan tituna suna goyon bayan jagoran juyin juya halin musulunci suna kuma yin allawadai da masu goyon bayan fitinannu a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Limamin yana fadar haka a khudubobinsa na sallar jumma’a a ‘Musallah na Imam Khomaini (q) dake birnin Tehran.
Kafin haka limamin yayi ishara da karatowar watan Ramadan mai al-farma da kuma muhimmancinsa, ya karanto kadan da cikin khudubar manzon Allah (s) dangane da falalar watan Ramadan, inda ya bayyana cewa saboda tsananin rahamar Allah da ke cikinsa numfashi da barci a cikin watan ma lada ake samu. Don haka yayi kira ga mutane su yi shirin shiga wannan wata mai al-farma na Ramadan don samun dimman alkhairi da ke cikinsa a duniya da lahira.
Limamin ya bayyana cewa a wani abu mai muhimmanci a cikin watan Ramadan da zai shigo, banda dadaren lailatul qadiri akwai ranar Qudus ta duniya wanda zai kasance a ranar 22 ga watan 12 na wannan shekara ta Iraniyawa.