Iran ta bukaci tarayyar turai ta sauya halayenta game da Tehran

Iran ta bukaci kungiyar tarayyar turai da ta sauya halayenta marasa kyau game da Tehran. Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ce dole ne

Iran ta bukaci kungiyar tarayyar turai da ta sauya halayenta marasa kyau game da Tehran.

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ce dole ne Tarayyar Turai ta sake duba halayenta “marasa inganci” ga Tehran.

Araghchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Cyprus, Constantinos Kombos, wanda kasarsa ke rike da shugabancin Tarayyar Turan.

Ya kuma soki hanyoyin da ba su dace ba na Tarayyar Turai kan Iran, musamman matakin da Majalisar Tarayyar Turai ta dauka kwanan nan na ayyana dakarun kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran (IRGC) a matsayin “kungiyar ta’addanci,” da kuma tsoma baki mara dalili da Majalisar ta yi a harkokin cikin gida na Iran.

Ministan harkokin wajen Iran ya shaida wa takwaransa na Cyprus cewa matsayin EU game da yankin, musamman kisan kare dangi a Gaza da laifukan da gwamnatin Isra’ila ta aikata kan kasashen yankin, ya saba wa doka da dokokin kasa da kasa.

A nasa bangaren Ministan harkokin wajen Cyprus Constantinos Kombos, ya yi maraba da bude wani sabon zagaye na tattaunawar nukiliya tsakanin Iran da Amurka, yana mai jaddada muhimmancin ci gaba da tattaunawa da rage tashin hankali.

Ya bayyana sha’awar kasarsa na bayar da duk wani taimako da ake bukata a wannan fanni.

A yayin tattaunawar ta wayar tarho, Mista Araghchi ya kuma yi wa takwaransa na Cyprus bayani game da sabbin abubuwan da suka faru a tattaunawar nukiliya tsakanin Tehran da Washington, Da aka gudanar tsakanin Iran da Amurka a Muscat, babban birnin Oman.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted