Tarayyar Afirka ta bukaci a dakatar da kisan gilla a Falasdinu

Tarayyar Afrika ta bukaci da a dakatar da kisan gilla da ake wa al’ummar Falasdinu. Sabon shugaban kwamitin kungiyar ne, Mahamoud Ali Youssouf ne, ya

Tarayyar Afrika ta bukaci da a dakatar da kisan gilla da ake wa al’ummar Falasdinu.

Sabon shugaban kwamitin kungiyar ne, Mahamoud Ali Youssouf ne, ya mika wannan kiran a lokacin bude taron shekara-shekara na kungiyar ta AU karo na 39.

Yau Asabar ne aka bude taron kungiyar a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha wanda kimanin shugabannin kasashe da gwamnatoci hamsin na nahiyar ke halarta.

Haka zalika an gayyaci Shugaban Hukumar Falasdinu da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya domin su yi jawabi a taron, da kuma Giorgia Meloni, Shugabar gwamnatin Italiya, a matsayin bakuwa ta musamman.

Rikicin gabashin DRC, da halin da ake ciki a Sudan wacce za’a tattauna batun mayar da ita a cikin kungiyar.

Daga cikin ajandar taron akwai batun rikicin Sudan ta Kudu, biyo bayan sake barkewar rikici tsakanin sojojin da ke biyayya ga Shugaba Salva Kiir da kungiyar SPLA-IO, wadanda ke biyayya ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Riek Machar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted