MDD ta yi Allah wadai da Isra’ila kan hana kai agajin jin kai Gaza

Majalisar Dinkin Duniya (MDD), ta yi Allah waidai da Isra’ila kan hana shigar da kungiyoyin agaji a zirin Gaza. Mai magana da yawun Majalisar Stéphane

Majalisar Dinkin Duniya (MDD), ta yi Allah waidai da Isra’ila kan hana shigar da kungiyoyin agaji a zirin Gaza.

Mai magana da yawun Majalisar Stéphane Dujarric, wanda ya ambaci Ofishin Kula da Harkokin Jin Kai na (OCHA), ya nuna cewa kungiyoyin MDD na kokarin daidaita ayyukan jin kai saidai hukumomin Isra’ila sun hana kungiyoyin da dama shiga Zirin.

An “samar da tallafi biyar,” yayin da hukumomin Isra’ila suka ki amincewa da wasu uku.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, kusan mutane miliyan 1.5 suna fuskantar wahalhalu.

A cewar hukumomin Falasdinu, yakin Gaza ya kashe mutane sama da 72,000 tare da raunata 171,000, wanda ya lalata kashi 90% na kayayyakin more rayuwa na fararen hula.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa ana bukatar kusan dala biliyan 70 domin sake gina Gaza.

Tun lokacin da aka fara aiwatar da tsagaita wuta a ranar 10 ga Oktoban 2025, akalla Falasdinawa 591 aka kashe kuma sama da 1,578 suka jikkata a hare-haren Isra’ila, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinawa a Gaza.

Hukumar Tsaron Farar Hula ta Gaza ta ba da rahoton cewa akwai gawawwaki kusan 8,000 wadanda suka kasance a binne a karkashin tarkacen gine-ginen da suka lalace a faɗin yankin Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted