Gwamnatin kasar Iran ta yi tir da kokarin da HKI take yi na kara mamayar yankunan falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan, da kuma ci gaba da kashe falasdinawa a yankina yamma da kogin Jordan da kuma Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghaei yana fadar haka a ranar Alhamis ya kuma kara da cewa HKI tana korar Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan tun da dadewa da nufin kara ginawa yahudawa yan shere wuri zauna gidaje a gonaki da kuma gidajen Falasdinawa da suke rusawa don yin hakan.
Baghaei ya kara da cewa dukkan abubuwan da sojojin HKI suke yi a yankin yamma da kogin Jordan ya sabawa dokokin kasa da kasa, kuma dole ne hukumomin da abin ya shafa a fagen kasa da kasa su dauki matakan da suka dace a kanta.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran yace, HKI tana aikata duk abubuwan da take yi a gaza da yankin yamma da kogin Jordan ne tare da goyon baya, amincewa da kuma tallafin kasashen Amurka da wasu kasashen Turai wadanda suka hana da Burtania da faransa da Jamus. Don haka su san cewa suna da hannu dumu dumu a zubar da jinin Falasdinawa a gaza da yankin yamma da kogin Jordan.