Sakataren Majalisar Tsaron Iran Admiral Ali Shamkhani ya ce; “Makamai Masu Linzami da muke da su, suna cikin jan layin da mu ka Shata da babu yadda za a yi tattaunawa akan makoarsu.”
Real Admiral Ali Shamkhani ya kara da cewa;makamai masu linzamin da Iran din take da su wani yanki ne na tsarin tsaron kasarta. Haka nan kuma ya ce; duk wani gigi na wuce gona da iri da za a yi akan Iran, to zai fuskanci mayar da martani mai tsanani. Har ila yau ya kara da cewa; A halin da ake ciki a yanzu, sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwana,don haka duk wani kuskuren lissafi zai fuskanci sakamako mai tsanani.
َAli Shamkhani ya kuma ce; Babu yadda za a yi ‘yan sahayoniya su iya kawo wa Iran hari, ba tare da cikakken goyon bayan Amurk aba.
Shugaban majalisar tsaron kasar ta Iran ya jaddada cewa; hanya ta hankali ita ce,a kaucewa faruwar yaki daga dukkanin bangarori, da kuma yin barazana da yaki.