Shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran Mohammad Islami ya bayyana cewa duk tare da matsin lamda da takurawar da kasashen yamma suka yi ta yi a kan Iran don hana ta ci gaba, amma abin mamaki hatta a wajemmu, mu masi aikin a wannan fannin shi ne, an sami ci gaba mai yawa a wannan fagen.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Muhammad Islami shugaban hukumar makamashin Nukliya na kasar Iran wato (AEOI) yana fadar haka a jiya Jumma’a a wani taro da daliban wasu Jami’o’I a birnin Mashad na arewa maso gabacin kasar.
Islami ya kara da cewa kasashen yamma musamman Amurka sun so su sami iko da kasar iran saboda ita ce ta biyu a duniya a yawan makamashin man fetur da iskar gas. Wannan arziki mai dimbin yawa ya rufe iadanunsu, ya kuma sa suka dauki matakai masu yawa don ganin sun sami iko da wannan kasar tamu.