Yahudawan Iran Sun Fito Tattakin Cika Shekaru 47 Da Nasara, Sun Kuma Yi Allawadai Da Amurka

Shugaban yahudawan Iran ya ce a ko wace shekara a ranar 11 ga watan Fabrayru suna fitowa tattaki don jaddada goyon bayansu ga hadin kan

Shugaban yahudawan Iran ya ce a ko wace shekara a ranar 11 ga watan Fabrayru suna fitowa tattaki don jaddada goyon bayansu ga hadin kan JMI da kuma goyon bayan tsarin musuluncin da ke tafiyar da kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto  Homayoun Sameyah Najafabadi shugaban kungiyar yahudawa a kasar Iran yana cewa, yahudawa a kasar Iran suna rayuwa cikin yenci karkashin shugabancin Sayyid Imam Aliyul Khaminaei, don haka suna fita tattakin 11 ga watan Febrayru don gode masa da kuma jaddada goyon bayansu gareshi.

JMI dai tana samun hadin kan mutanen kasar, duk tare da bambance bambance da ke tsakanin su na kabilu da addinai da kuma bangarori. Musulmi da yahudawa da kiristoci a Iran suna zauna lafiya a tsakaninsu, kuma kananan addinai da mazhabobi suna da kujeru a majalisar dokokin kasar inda suke wakiltan mutanensu a majalisar.

Najafabadi ya ce yana fatan tsarin JMI ya wanzu na daruruwan shekaru masu zuwa, saboda su basa fuskantar wata matsala ko guda a kasar duk tare da cewa suna daga cikin kananan addinai a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted