Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaei ya godewa mutanen Iran kan fitowarsu jiya Laraba don nuna goyon bayansu da kuma halattar bukukuwan cika shekaru 47 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar.
Shafin yanar gizo na Jagoran ya bayyana cewa ya bayyana godiyarsa ne a wani faifen bidiyo da ya aikawa kafafen yada labaran kasar suka yada. Ya ce mutanen kasar Iran sun kungiya makiya, sun kuma sanyasu debe kauna daga mika kai ga muradunsu.
Jagoran ya kara da cewa fitowar mutane a jiya Laraba zai kara daukaka kasar Iran da kuma mutanen kasar, kuma abinda suka aikata a jiya 22 ga watan Bahman wani babban al-amari ne wanda zai wanzu a tarihin kasar.
Daga karshe Imam Khaminei ya yi kira ga mutanen kasar su kiyaye hadin kan da ke tsakaninsu, don yin haka ne zai kara daukaka kasar ya kuma hana makiya kodayin mamaye kasar.
A jiya Laraba ce miliyon mutanen kasar Iran a birane da kauyuka a larduna da kuma birnin Tehran suka fito kan titunan kasar inda suke nuna goyon bayansu ga JMI da kuma yin allwadai da Amurka da HKI kan mummunan manufofinsu kan kasar.