Shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan ya godewa mutanen kasar Iran dangane da fitowarsu kan titunan birane da kauyukan kasar a ranar 22 ga watan Bahman ranar nasarar juyin juya halin musulunci a kasar.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka ne a safiyar yau Alhamis a wani jawabinda da gabatar a lardin Golistan na arewacin kasar.
Shugaban ya kara da cewa: Na gode sosai dangane da fitowar mutanen kasar don goyon bayan da kuma murnar nasarar juyin juya halin musulunci a kasar shekaru 47 da suka gabata. Yace mutanen sun fito kan titunan kasar don goyon bayan tsarin siyasar da ke gudanar da kasar, duk tare da farfagandar makiya na nisantar da su daga fitowa.
A wani bangare a jawabinsa shugaba Pezeshkiyan ya bayyana cewa, shuwagabanni, da yan siyasa a kasar suna da babban nauyi a kansu na aiki wa mutanen kasar wadanda suka nuna cewa ba wanda ya isa ya yaudaresu.
Yace dole ne manufar gwamnati ta kasance warware matsalolin tattalin arzikin da mutanen kasar suke cika, amma hakan ba zai yi ba sai tare da hadin kan mutane da kuma goyon bayansu. Ya ce bai kamata mutanen jami’an gwamnatin kasar su kyale mutane a cikin halin da suke ciki ba.