Wani dan majalisar dokokin kasar Amurka ya gabatar da doka a majalisar wakilan kasar tare da bukatar kakabawa wasu daddaikun mutane da kungiyoyi a tarayyar Najeriya, a shirin Amurka na taimakawa kiristocin Najeriya.
Jaridar Leadership ta Najeriya ta bayyana cewa Riley Moore (dan majalisa mai wakiltan yammacin jihar Virginia) ne ya gabatar da dokar wacce aka bawa suna ( ‘the Nigeria Religious Freedom and Accountability Act of 2026’) wato dokar yencin indini a najeriya ta shekara ta 2026. Har’ila yau ya sami goyon bayan yan majalisar wakilai Chris Smith (mai wakiltan -New Jersey) duk sun bukaci amincewa majalisar wakilan kasar amincewa da wannan dokar.
Dokar ta ambaci sunan tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanato Rabiu musa Kwakwaso da kuma kungiyar Fulani ta miyetti Allah ta makiyaya da kuma miyatti Allah kautal Hore a matsayin wadanda dokar take nufi da takunkuman.
Dokar ta bukaci hukumar baitul malin Amurka ta yi nazarin yiyuwar dora takunkuman tattalin arziki kan wadanda aka ambata. Sannan ma’aikatar harkokin waje ta yi nazarin ta kuma gano wadanda ta kira yan ta’adda Fulani wadanda ake zargi da ayyukan ta’addanci.
Banda haka dokar ta bukaci a tallafawa kabilun tsakiyar Najeriya tare da amfani da kungiyoyin agaji masu zaman kansu. Tare da aiki tare da gwamnatin Najeriya don daukar mataki a kansu.