Duniya na taya Iran murnar cika shekaru 47 na nasarar juyin juya hali

Shugabannin kasashen duniya da manyan jami’ai na ci gaba da aikawa da sakonnin fatan alheri ga Iran a game da bikin cika shekaru 47 da

Shugabannin kasashen duniya da manyan jami’ai na ci gaba da aikawa da sakonnin fatan alheri ga Iran a game da bikin cika shekaru 47 da samun nasarar Juyin juya halin Musulinci.

Shugaban Nicaragua Daniel Ortega ya fitar da wata sanarwa yana taya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, Shugaba Masoud Pezeshkian, da kuma al’ummar Iran murnar cika shekaru 47 da nasarar juyin juya halin Musulunci.

Shi ma Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani, Firaminista kuma Ministan Harkokin Waje na Qatar, ya aika da irin wannan sako ga Shugaba Pezeshkian.

A wani sakon na daban, Mahdi al-Mashat, Shugaban Majalisar Siyasa ta Yemen, shi ma ya aika da sakon taya murna ga Shugaba Pezeshkian a a bikin cika shekaru 47 da nasarar juyin juya halin Musulunci.

Shi ma Ministan Harkokin Waje na Indiya Subrahmanyam Jaishankar, ya aike da sako irin haka ga takwaransa na Iran Abbas Araghchi a shafin X, yana taya shi, da gwamnatin Iran, da kuma al’ummar kasar murnar cika shekaru 47 da juyin juya halin Musulunci.

A daya bangaren kuma Ofishin shugaban Kazakhstan shi ma ya wallafa wani sako a shafin X, yana ambaton Shugaba Kassym-Jomart Tokayev, yana taya Iran murnar zagayowar ranar juyin juya halin Musulunci.

A gefe guda kuma, shugaban Pakistan Asif Ali Zardari shi ma ya aika da sako a lokacin bikin cika shekaru 47 na juyin juya halin Musulunci, yana taya Ayatollah Khamenei da gwamnatin Iran murna, yayin da yake yi wa al’ummar Iran fatan ci gaba, wadata, da zaman lafiya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres shi ma ya fitar da sako a hukumance yana taya Shugaba Pezeshkian da al’ummar Iran murnar zagayowar ranar juyin juya halin Musulunci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted