Rahotanni sun bayyana cewa yan kasar Burtania fiye da 2,000 ne suka yi yaki kafada da kafada da sojojin HKI a kissan kiyashin da suka aikata a zirin Gaza a cikin shekaru bityu da suka dauka suna kisa a gaza.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar ‘Declassified UK’ tana fadar haka a jiya laraba.
Labarin ya kara da cewa Declassified Uk ta samu labarin ne daga ‘Freedom of Information Request’ wanda aka gabatarwa gwamnatin HKI. Kafin haka dai gwamnatin HKI ta bada rahoton cewa yan kasar Burtania 54 kacal suka shiga yakin kisan kiyashin falasdinawa a gaza daga shekara ta 2023 zuwa 2024.
Amma sabon kididdigan da aka samu ya nuna cewa yan kasar Burtania, wadanda kuma suke da passport na HKI 1,686 ne suka shiga yaki a HKI suka kuma kashe Falasdinawa a gaza. Sannan wasu 383 kuma wadanda suke da yan passport da kasashe uku, wadanda suka hada da HKI da Burtania ne, suka shiga yakin kisan kare dangin. Sojojin kimani 50,000 ne suka shiga yakin kisan kiyashi a gaza a bangaren HKI.
Labarin ya kara da cewa a shekarar da ta gabata wasu yan kasar ta Burtania sun shigar da kara mai shafi 240 a gaban yansandan burtania tare da zargin yan kasar Burtania 10 da hannu wajen kashe fararen hula da kuma jami’an agaji a zirin gaza..