Kotu Ta Bukaci Hukumar ICE Ta Sallami Yaro Dan Shekara 5 Da Mahaifinsa Da Ta Kama A Miniapolis

Wani alkali a Amurka ya bada umurnin sakin yaro dan shekara 5 da mahaifinsa wadanda jami’an shige da fice na Amurka wata (the Immigration and

Wani alkali a Amurka ya bada umurnin sakin yaro dan shekara 5 da mahaifinsa wadanda jami’an shige da fice na Amurka wata (the Immigration and Customs Enforcement (ICE)

Suka kama yan makonnin da suka gabata. Suka kuma ci gaba da tsaresu a jihar Texas.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto alkalin mai shariaFred Biery  yana yanke hukunci a jiya Asabar. Ya kuma kara da cewa da akwai alamun akwai rashin amini da tausayi a cikin jami’an tsaron kasar.

Dangane da shirin gwamnati na korar wasu bakin haure a Amurka kuma mai sharia Fred Biery ya ce gwamnati tana iya yinsa ta hanyar barin kowa ya zabi komawa kasar da ya fito ba tare da an yi amfani da karfi a kansa ba.

Ko kuma a bi wata hanya wacce babu nuna karfi a cikinsa.

Fadar White house dai tace tana da shirin kama bakin haure kimani 3000 ko wace rana don fitar da su daga kasar Amurka, kuma wannan shirin zai ci gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted