Rahotannin da suke fitowa daga gabashin kasar ta DRC a yankin dake karkashin ‘yan tawaye, suna cewa, a kalla mutane 200 ne su ka rasa rayukansu saboda saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya, da ya haddasa zaizayar kasa a wajen hako ma’adanan Coltan na Rubaya.
Yankin da lamarin ya faru dai yana a karkashin kungiyar ‘yan tawaye ta M23 da ta kwace iko da shi tun a 2024.
Mai Magana da yawun gwamnan yankin Kivu ta Arewa da ‘yan tawayen su ka nada, Lumumba Kambere Muyisa ya fadi cewa: Daga cikin wadanda su ka rasa rayukan nasu da akwai mata da kananan yara da kuma masu hako ma’adanai.
Tun a ranar Juma’a ne Mahukunta a kasar DRC su ka ce, mutane fiye da 200 sun kwanta dama sanadiyar ruftawar wani ramin hako ma’adanin “Coltan”dake gabashin kasar.
Sanarwar ta ce, an sami afkuwar hatsarin ne a ranar Larabar da ta gabata, sai dai ba a iya samun cikakken adadin mutanen da su ka rasu ba sai a jiya Juma’a.
Wurin hako ma’adanin da lamarin a faru shi ne Robaya wanda yake kunshe da kaso 15% da dukkanin ma’adanin “Coltan” da ake da shi a duniya. Kamfanonin da suke kera wayoyin hannu da kuma na’ura mai kwakwalwa suna amfani da shi a kere-kerensu.
Wani jami’in gwamnati ya fada wa manema labaru cewa; alkalumma sun tabbatar da cewa wadanda su ka rasa rayukan nasu, sun kai 227, sun kuma hada mata da kananan yara.
Gabashin DRC dai yana cike da ma’adanan da Allah ya shimfida kwance a karkashin kasa, da wasu daga cikinsu su ne mafi yawa da ake da su a duniya.
Tun dai aka dakatar da gudanar da dukkanin ayyukan hako ma’adanai a cikin wannan yankin, tare da dauke mutanen yankin da lamarin ya rutsa da su zuwa tudun mun tsira.
MDD ta yi zargin cewa, kungiyar ta M23 tana dibar albarkatun da suke a cikin yankin domin samar da kudaden gudanar da ayyukanta na yaki.