Guinea Bissau: An Saki Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasa Bayan Da Ya Kwashe Watanni A Tsare

Shugaban ‘yan hamayyar siyasar kasar Gunea Bissau, Domingos Simoes Pereira ya shaki iskar ‘yanci a ranar Juma’a bayan zaman gidan yari na watanni. Simones Pereira

Shugaban ‘yan hamayyar siyasar kasar Gunea Bissau, Domingos Simoes Pereira ya shaki iskar ‘yanci a ranar Juma’a bayan zaman gidan yari na watanni.

Simones Pereira yana cikin manyan ‘yan siyasar kasar da aka kama bayan juyin mulkin da sojoji su ka yi a cikin watan Nuwamba, da hakan ya kawo karshen mulkin shugaba Umaru Sissoco,Embalo.

Sojojin da su ka hau karagar mulkin kasar, sun sanar da cewa sun hana afkuwar zubar da jini a tsakanin jam’iyyun dake adawa da juna,kuma za su ci gaba da tafiyar da kasar har na tsawon shekara daya.

Bayan sakin nashi, sojojin kasar sun kuma hana wa , Domingos Simoes Pereira sake shiga harkar zabe.

A lokacin zaben da aka gudanar dai,  kowane daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar Fernando Dias, da Embalo ke goyawa baya da kuma Pereira sun rika cewa shi ne wanda ya lashe zabe.

Tun bayan samun ‘yancin kasar Guinea Bissau daga ‘yan mulkin mallakar kasar Portugal a 1974,  ta rika fuskantar  juyin Mulki daga lokaci zuwa lokaci. Sau daya a tarihin wannan kasar aka sami shugaban kasar da ya kammala wa’adinsa na Mulki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted