Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyanawa kasar Indiya ta dakatar da sayan mai daga kasar Iran ta koma sayan man fetur a hannun kasar Venezuela kuma tuni yayi barazanar daukar mataki kan kasar na kakaba mata haraji mai nauyi idan bata daina sayan mai daga hannun kasar iran ba,
Sai dai new dalhi ta yi watsi da barazanar kuma ta sanar cewa shugaban Amurka bashi da hakkin tantance mata kasar da ta kamata ta yi huldar kasuwanci ko wata danganta ka da ita.
A fili trump yake bayyana cewa ya samu cikakken ikon kula da ma’aikatar man fetur din kasar Venezuela bayan da dakarun sojin Amurka suka sace shugaban kasar ta kudancin Amurka Nicolas Maduro
Wani masanin sharia ya bayyana cewa ikirarin da Trump yayi na iko da albarkatun man fetur din kasar Venezuela ya saba ma doka,