Rahotanni daga birnin bagadaza sun nuna cewa Jam’iya mafi rinjaye a majalisar dokokin kasar iraqi ta nuna goyon bayanta ga Nuri Maliki a matsayin sabon fira ministan kasar duk da barazanar da shugaban Amurka Donald Trump yayi, da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar
a cikin wani bayani da suka fitar gamayyar jamiyun da yan shia ke da rinjaye a majalisar sun nuna goyon bayansu ga Nuri maliki a matsayin dan takararsu na mukamin fira ministan kasar ta iraki.
A yan kwanakin nan ne shugaban Amurka yayi barazanar dakatar da duk wani taimako ga kasar Iraqi idan ta zabi Nuri Al-maliki a matsayin sabon fira ministan kasar dake yamamcin asiya.
Ana sa bangaren tsohon fira ministan kasar iraki Nuri Al-maliki yayi watsi da barazanar da Trump yayi kuma ya bayyanata a matsayin shiga shugular cikin gidan kasar Iraqi .