Rahotanni sun bayyana cewa dubban masu zanga-zanga ne suka hau kan tituna a kasashen turai domin nuna goyon bayansu ga Alummar falasdinu da kuma yin tir da gwamnatin isra’ila na ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakaninta da kungiyar Hamas kan Gaza.
Akalla mutane dubu 10 ne suka yi macin a fadin birnin London da stokholm a jiya asabar domin nuna goyon bayansu ga alummar falasdinu, kuma sun yi tir da ci gaba da kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a gaza, duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma, kuma sun bukaci kasashen turai su dakatar da siyar da makamai ga isra’ila.
yar majalisar birtaniya Zahra sultana da john macdonnell sun halarci zanga-zangar tare da wani babban likita dan birtaniya da falasdinu Ghassan Abu Sitta wanda ke aiki a yankin gaza.
Ma’aikatar lafiya ta yankin falasdinu ta bayyana cewa kimanin falasdinawa 17 ne Isra’ila ta kashe tare da jikkata wasu 49 a cikin sao’i 48 da suka gabata .