IRGC Ya Musanta Cewa Sojojin Ruwa Na Amurka Sun Zo Yankin Ne Don Barazana Kawai

Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ya yi watsi da maganar cewa sojojin ruwa na Amurka sun zo yankin tekun

janar wahidi

Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ya yi watsi da maganar cewa sojojin ruwa na Amurka sun zo yankin tekun farisa ne don yakin farfaganda, don haka dakarunsa a shirye suke su tunkari duk wani hari kan kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto Burgedia Janar Ahmad Vahidi yana fadar haka a lokacinda yake hira da fafafen yada labarai dangane da samuwar sojojin Amurka a yankin.

Janar Vahidi ya kara da cewa a wannan halin su basa daukar tsaron kasar Iran da wasa, don yakin tada hankalin mutane ma bangare ne na yaki, don haka mutane su ci gaba da ayyukansu nay au da kullam, amma dakarun kare juyin juya halin musulunci ba zasu taba gafala ko da na kebtawar idone kan sojojin kasar Amurka da suke zo yankin ko suke yankin. Haka ma sauran kawayensu a yankin.

Ya kuma kammala da cewa sojojin Iran a shirye suke fiye da yadda suka aiwatar da yakin kwanaki 12, kuma akwai yiyuwar makiya zasu sake yin kuskure, irin wanda suka yi baya, a nan ne zasu yabawa aya zaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted