Iran: An Bude Babbar Cibiyar Farko Ta Kirkirarriyar Fasaha Da Tattara Bayanan Ilimin Kimiyya

A yau Laraba ne dai aka bude cibiyar kirkirarriyar fasaha da tattara bayanan kimiyya saboda biyan bukatun jami’o’in kasar wajen aiwatar da aikace-aikace da nazarce-nazarce. An yi kwarya-kwaryar bikin bude cibiyar ne wanda ya sami halartar malaman jami’oi da masana kirkirarriyar fasahar a cikin jami’ar Shahid Baheshti. Shugaban Babbar cibiyar fasaha ta kasar Iran Mehrshad […]
Gwamantin Donald Trump Ta Kara Yawan “Yan Kasashen Da Za Ta Hana Wa Shiga Amurka

Sabbin kasashen da gwamnatin Donald Trump sun kunshi, Burkina Faso, Mali, Niger, Sudan Ta Kudu da Syria A jiya Talata ne dai Amurkan ta sanar da Karin wadannan kasashen biyar da baki daya ana hanawa ‘yan kasar zuwa Amurka, sai kuma wasu Karin kasashe 15 da aka haramcin da aka wa ‘yan kasar zuwa Amurka, […]
Kaso 90% Na Hemomin ‘Yan Hijira A Gaza Sun Nutse A Cikin Ruwa

Hukumar Agaji ta sanar da cewa sanadiyyar saukar ruwan sama mai yawa a yankin Gaza, Falasdinawa 17 sun rasa ransu, kuma kaso 90% na wuraren da aka warewa ‘yan hijira sun jike a cikin ruwa. Daga cikin wadanda su ka rasa rayukan nasu saboda sanyi da akwai kananan yara 4, sauran kuwa sun rasa rayukansu […]
Benin: Ana Ci Gaba Da Farautar Wadanda Su Ka Jagoranci Juyin Mulkin Da Bai Yi Nasara Ba

Majiyar hukumar shari’a ta kasar Benin ta ce, ya zuwa yanzu an kama mutane 30, mafi yawancinsu sojoji kuma ana tsare da su a kurkuku daga jiya 16 Disamba, bayan da aka gabatar da su a gaban kotun kasar mai shari’ar ta’addanci da kuma yi wa tattalin arziki ta’annati a jiya Talata 16 ga watan […]
Hukumar Makamashi Ta Duniya: Neman Gawayin Kwal ( Coal) Ya Kai Koli A Cikin Wannan Shekara Ta 2025

Hukumar makamashi ta duniya ta sanar da cewa yadda ake neman gawayin kwal a duniya a wannan shekarar ta 2025 mai karewa shi ne mai yawa a tsawon tarihi, domin ya haura na 2024. Sanarwar ta ce a shekarun baya an sami koma bayan neman gawayin na Kwal saboda an samo wasu hanyoyi na samar […]
Mafarkin Nijeriya Na Zuwa Gasar Kofin Duniya Na Dab Da Cika

Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya ta tabbatar da cewa ta fara bincike kan zargin amfani da dan wasan da bai cancanta ba a wasan da Nijeriya ta buga da kasar Dimokuradiyar Congo a lokacin wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Duniya ta FIFA ta shekarar 2026, wani abu da zai iya sake bude hanyar […]
Venuzuwela Ta Kai Karar Amurka Gaban Kwamitin Tsaron Na MDD

Ministan harkokin wajen kasar Venuzuwela Ivan gil ya bayyana cewa sun aike da wasikar koke ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya wanda a ciki suka yi tir da kwace tankar man venuzuwela da kasar Amurka ta yi, Babban jami’an na venuzuwela yace kasarsa za ta ci gaba da yin amfani da hakkinta na kare […]
Iran Ta Gayyaci Jakadan Kasar Cyprus Kan Kalaman Da Ta yi Kan Tsibiran Nan Guda 3

Rahotanni sun bayyana cewa iran ta kirayi jakadan kasar Cyprus a nan birnin Tehran domin nuna matukar rashin jin dadinta game da kalaman baya bayan nan da kasar ta yi kan martabar kasar iran, musamman kan tsibiran nan guda 3 dake tekun fasha. Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta kira jakadan Cyprus a Tehran petros […]
Shugaban Ansarullah Yayi Kira Ga Musulmi Da su Dauki Mataki Kan Cin Zarafin Alkur’ani A Amurka

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yamen Abdul malik Al’huthi yayi tir da cin zarafin Alkur’ani maigirma da aka yi a baya-bayan nan a kasar Amurka inda yayi kira ga dukkan musulmin duniya da su dauki tsattsauran mataki don kare martabarshi. A cikin bayanan da ya yi a jiya talata ya bayyana cin zarafin a matsayin […]
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Kai Ziyara Rasha Domin Tattaunawa Kan Muhimman Batutuwa

Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya isa birnin mosko tare da muhimmiyar tawaga dake mara masa baya inda zasu tattauna da mahukumta kasar rasha kan muhimman batutuwa da suka shafi dagantakar dake tsakaninsu Wannan ziyarar tana nuna irin muhimmanci hadin kai tsakanin iran da rasha adaidai lokacin da ake […]
Iran : Duk da wahalhalun da ake ciki, akwai nasarori masu yawa_Jagora

Jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa duk da wahalhalun dake akai a kasar, akwai nasarorin masu yawa da ake samu. Jagoran ya bayyana hakan ne a taron tunawa da shahidai 5,580 na Lardin Alborz, inda yake cewa: “Duk da wahalhalun da ake fuskanta a yanzu, kasarmu tana […]
Araghchi ya jaddada kudurin Iran na kare hakkinta na nukiliya bisa yarjejeniyar NPT

Ministan harkokin wajen Iran, Abbass Araghchi, ya sake jaddada kudurin kasar na kare hakkokinta na nukiliya bisa ga yarjejeniyar hana yaduwar makamman nukiliya ta duniya NPT. A yayin wata ganawa da kwararrun Rasha a birnin Moscow, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya sake jaddada kudurin Iran na kare hakkoƙinta da muradunta na halal, bisa […]
ICC Ta Yi Watsi Da bukatar Isra’ila Na Neman Soke Umarnin Kama Netanyahu

Ofishin daukaka kara na Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ya yi watsi da hujjojin Isra’ila da ke kalubalantar ingancin binciken da ta gudanar kan laifukan da aka aikata a Gaza bayan yakin Isra’ila a yankin Gaza da aka kewaye. Wannan shawara ta zo ne, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike […]
WHO ta yi gargadi game da sake fuskantar barazanar malaria

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadin cewa za a iya fuskantar mummunan barazanar zazzabin cizon sauro, musamman a nahiyar Afirka. Yara sun fi fuskantar rauni, yayin da ake fuskantar cikas ga kawar da cutar. Kasashen da suka fi fuskantar mummunan mace-mace da ke da alaka da zazzabin cizon sauro, a Afrika su […]
Venezuela ta soki Amurka kan hana shige da ficen man fetur a kasar

Gwamnatin Venezuela ta yi Allah wadai da umarnin da Amurka ta bayar na sanya abin da ta kira “haramta shiga da fitar da man fetur gaba daya” dake da alaka da kasar, tana mai zargin Washington da karya dokokin kasa da kasa da kuma kara ruruta rikici mai hatsari a yankin Caribbean. A cikin wata […]