Ministan harkokin wajen Iran, Abbass Araghchi, ya sake jaddada kudurin kasar na kare hakkokinta na nukiliya bisa ga yarjejeniyar hana yaduwar makamman nukiliya ta duniya NPT.
A yayin wata ganawa da kwararrun Rasha a birnin Moscow, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya sake jaddada kudurin Iran na kare hakkoƙinta da muradunta na halal, bisa ga tanade-tanaden Yarjejeniyar ta (NPT).
Araghchi ya je Moscow a ranar Talata, don tattaunawa kan huldar dake tsakanin kasashen biyu da ci gaban da ake samu a yanayin kasa da kasa.
Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana matsayin Tehran a hukumance kan batutuwan da suka shafi zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa.
Ya jaddada muhimmancin shirin nukiliyar Iran, yana mai nuna tsarin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauka a cikin shekaru ashirin da suka gabata.
Araghchi ya danganta halin da ake ciki a yanzu da keta dokokin da Amurka ta yi a alkawuran da ta dauka ciki har da janyewa daga yarjejeniyar nukiliya ta 2015 da kuma shirin kai hari kan kasar a watan Yunin 2025.
Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada bukatar gaggawa ta “karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu ‘yanci,” a cikin hukumomin kasa da kasa kamar Majalisar Dinkin Duniya, BRICS, da Kungiyar Hadin Kan Shanghai (SCO).