A yau Laraba ne dai aka bude cibiyar kirkirarriyar fasaha da tattara bayanan kimiyya saboda biyan bukatun jami’o’in kasar wajen aiwatar da aikace-aikace da nazarce-nazarce.
An yi kwarya-kwaryar bikin bude cibiyar ne wanda ya sami halartar malaman jami’oi da masana kirkirarriyar fasahar a cikin jami’ar Shahid Baheshti.
Shugaban Babbar cibiyar fasaha ta kasar Iran Mehrshad Naf’i, ya bayyana cewa; manufar bude wannan cibiyar shi ne bayar da dama ga kwararru masu bincike na nazarce-nazarce su gudanar da ayyukansu, domin biyan bukar da ake da ita a cikin kasa a wannan fagen. Haka nan kuma malamai da daliban jami’oi ne za su kasance a sahun gaba wajen cin moriyar wannan cibiyar.
Daga nan zuwa shekara mai zuwa ana sa ran bude wasu sabbin cibiyoyin na kirkirarriyar Fasaha da tattara bayanan ilimin kimiyya har guda 5 a wasu tsangayoyin na ilimi.