Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya isa birnin mosko tare da muhimmiyar tawaga dake mara masa baya inda zasu tattauna da mahukumta kasar rasha kan muhimman batutuwa da suka shafi dagantakar dake tsakaninsu
Wannan ziyarar tana nuna irin muhimmanci hadin kai tsakanin iran da rasha adaidai lokacin da ake samun canji yanayi da kuma kalubalen da ake fuskanta na kasa da kasa.
A lokacin ziyarar tasa an tsara cewa Araqchi zai gana da sargi lavrov ministan harkokin wajen kasar ta Rasha, inda za su tattauna kan batun dake da alaka da dangarkatarsu da sauran muhimman batutuwa da kasashen biyu suka yi tarayya akai.