Rahotanni sun bayyana cewa iran ta kirayi jakadan kasar Cyprus a nan birnin Tehran domin nuna matukar rashin jin dadinta game da kalaman baya bayan nan da kasar ta yi kan martabar kasar iran, musamman kan tsibiran nan guda 3 dake tekun fasha.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta kira jakadan Cyprus a Tehran petros Nacouzis ne a jiya talata bayan da suka fitar da wani bayani na hadin guiwa da hadaddiyar daular larabawa na ikirarin da suka yi kan tsibiran nan dake tekun fasha wato tumbu babba da tumbu karami da kuma Abu musa.
Tsibiran guda 3 wani bangare ne na kasar iran wanda tarihi ya tabbatar da su da babu jayayya akai, da ma wasu takardu dake hannun iran da ma wasu bangarorin a duniya. amma duk da haka hadaddiyar daular larabwa ta ci gaba da ikirari akan tsibiran.
Tsibiran sun kasance karakashin ikon birtaniya a shekara ta 1921 sai dai a ranar 30 ga watan nuwamba na shekara ta 1971 kwanaki biyu bayan ficewarta hadaddiyar daular larabawa ta zama dunkulalliyar kasa a hukumance, kuma aka tabbatar da ikon mallakar tsirbiran ga kasar Iran.