Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadin cewa za a iya fuskantar mummunan barazanar zazzabin cizon sauro, musamman a nahiyar Afirka.
Yara sun fi fuskantar rauni, yayin da ake fuskantar cikas ga kawar da cutar.
Kasashen da suka fi fuskantar mummunan mace-mace da ke da alaka da zazzabin cizon sauro, a Afrika su ke inji rahoton
A shekarar 2024, an sake fuskantar dawowar zazzabin cizon sauro a duniya, inda aka kiyasta mutuwar mutane 610,000.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta jaddada cewa Afirka ta kasance yankin da cutar ta fi shafa, wanda ya kai kashi 95% na mace-mace masu nasaba da cutar.
Kuma wannan yanayin da ba a saba gani ba yana shafar yara ‘yan kasa da shekara biyar, wadanda ke wakiltar kusan kashi 76% na mace-macen da aka samu a nahiyar.
Kasashen na Afrika da lamarin ya fi shafa su ne a sahun gaba Najeriya, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC), da Nijar.
Najeriya ce ke da mafi yawan mace-macen da ke da alaƙa da zazzabin cizon sauro, inda kashi 31.9%, sai Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da kashi 11.7%, sannan Nijar da kashi 6.1%.
Wannan na da nasaba ne sakamakon gibin kudi mai yawa.
A shekarar 2024, an ware dala biliyan 3.9 don shawo kan cutar maleriya, kasa da rabin abin da aka sa gaba na dala biliyan 9.3 a shekarar 2025.