Shugaban Ansarullah Yayi Kira Ga Musulmi Da su Dauki Mataki Kan Cin Zarafin Alkur’ani A Amurka

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yamen Abdul malik Al’huthi yayi tir da cin zarafin Alkur’ani maigirma da aka yi a baya-bayan nan a kasar Amurka

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yamen Abdul malik Al’huthi yayi tir da cin zarafin Alkur’ani maigirma da aka yi a baya-bayan nan a kasar Amurka inda yayi kira ga dukkan musulmin duniya da su dauki tsattsauran mataki don kare martabarshi.

A cikin bayanan da ya yi a jiya talata ya bayyana cin zarafin a matsayin babban laifi kan addini mafi girma a fadin kasa , ya jaddada cewa wannan wani bangare ne na yakin da ake yi da musulunci da kasar Amurka ke jagoranta tare da birtaniya isra’ila da sauran kawayensu a gabashi da yammacin duniya.

Huthi ya yi gargadin cewa rashin kulawa da yin shiru kan irin wanan cin mutunci  yana karfafa makiya ne kawai kuma yana nuna irin raunin musulmi a bangaren Imani da akida da kuma martabarsu.

Daga karshe shugaban yayi kira ga dukkan alummar Yamen da su gudanar da gagarumar zanga-zanga a ranar jumaa mai zuwa domin kare martabar Alur’ani mai tsarki da sauran wurare masu tsarki na musulunci da kuma nuna goyon bayan alummar falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted