Hukumar Makamashi Ta Duniya:  Neman Gawayin Kwal ( Coal) Ya Kai Koli A Cikin Wannan Shekara Ta 2025

Hukumar makamashi ta duniya ta sanar da cewa yadda ake neman gawayin kwal a duniya a wannan shekarar ta 2025 mai karewa shi ne mai

Hukumar makamashi ta duniya ta sanar da cewa yadda ake neman gawayin kwal a duniya a wannan shekarar ta 2025 mai karewa shi ne mai yawa a tsawon tarihi, domin ya haura na 2024. Sanarwar ta ce a shekarun baya an sami koma bayan neman gawayin na Kwal saboda an samo wasu hanyoyi na samar da wutar lantarki.

Rahoton shekara-shekara na wannan hukuma ya ambaci cewa yawan kwal din da aka bukta a wannan shekarar ya kai ton biliyan8.85%, kuma dalilai ne masu yawa su ka hadda hakan, daga ciki har da sabuwar siyasar makamashi ta Amurka.

Sai dai kuma rahoton ya ce, da akwai yiyuwar a sami koma bayan bukatuwa da gawayin na gwal daga nan zuwa 2030, da zai koma zuwa yadda ya kasance a 2023.

Wani bayani na hukumar ta bayyana cewa; An sami koma bayan bukatuwa da gawayin gwal ne a 2023, saboda yadda ake amfani da wasu hanyoyin samar da wutar lantarki, da su ka hada fasahar Nukiliya da kuma Gas.

Kasar China ce dai ta daya a duniya wajen sarrafa gawayin gwal a matsayin makamashi, saboda ita kadai ce take sayen kaso 56% na wanda ake fitarwa da duniya, duk da cewa tana amfani da hasken rana da iska wajen samar da makamashin.

Ita kuwa kasar Indiya bukatarta da gawayin na gwal ya ragu,a karo na uku a cikin shekaru 50.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted