Sabbin kasashen da gwamnatin Donald Trump sun kunshi, Burkina Faso, Mali, Niger, Sudan Ta Kudu da Syria
A jiya Talata ne dai Amurkan ta sanar da Karin wadannan kasashen biyar da baki daya ana hanawa ‘yan kasar zuwa Amurka, sai kuma wasu Karin kasashe 15 da aka haramcin da aka wa ‘yan kasar zuwa Amurka, kayayadajje ne. Wadannan kasashen sun hada Nigeria,Senegal, Ivory coast da Tanzania.
Haka nan kuma masu dauke da passport din Falasdinu an hana su shiga cikin Amurka baki daya.
Amurkan ta ce dalilan tsaro ne su ka sa ta dauki wadannan matakan na haramtawa ‘yan kasashen Afirka da dama shiga cikinta, tare da bayyana wasu dalilan da su ka hada cin hanci da rashawa a wadannan kasashen da kuma rikice-rikice.
Sai dai kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun yi suka akan cewa matakin zai iya hana wadanda su ka cancanta samun mafaka, kamar mutanen Afghanistan da sun taimaka wa sojojin Amurka.
Wasu kuwa suna ganin cewa matakanin na Amurka an dauke shi ne bisa la’akari da kasashen da mutanen su ka fito, da kuma nuna wariyar launin fata da jin fifiko na fararen fata.