Gwamnatin Venezuela ta yi Allah wadai da umarnin da Amurka ta bayar na sanya abin da ta kira “haramta shiga da fitar da man fetur gaba daya” dake da alaka da kasar, tana mai zargin Washington da karya dokokin kasa da kasa da kuma kara ruruta rikici mai hatsari a yankin Caribbean.
A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, Mataimakiyar Shugaba Delcy Rodríguez ta ce matakin Shugaba Donald Trump ya yi kama da “barazana mai tsanani” wanda ya karya ka’idojin cinikayya cikin yanci da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa.
Ta bayyana matakin a matsayin wani yunkuri na shake tattalin arzikin Venezuela da kuma kwace iko da albarkatun kasar.
Martanin ya zo ne kwana guda bayan da Trump ya sanar da cewa ya ba da umarnin “haramta duk wani shige da fice jiragen ruwa na dakon man fetur gaba daya” daga Venezuela, yayin da sojojin Amurka ke ci gaba da mamaye gabar tekun arewacin kasar a Tekun Caribbean.
Caracas ta kira matakin da “abin takaici,” tana zargin Trump da yin kamar man fetur, filaye da ma’adanai na Venezuela mallakar Amurka ne.
Sanarwar ta ce “Trump ya dauka cewa albarkatun Venezuela mallakarsa ne,” in ji sanarwar.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya yi gargadin cewa matsin lamba zai kara tsananta har sai Caracas ta dawo da “dukkan man fetur, filaye, da sauran kadarorin da suka sace daga gare mu a baya.”
Wannan furucin ya yi kama da na nuna yadda Venezuela ta mallaki kadarorin Amurka a shekarun da suka gabata.
Trump ya kuma yi ikirarin cewa sojojin Amurka za su iya kai hare-haren kasa a yankin Venezuela.
Washington ta ce matakanta na nufin wargaza abin da ta bayyana a matsayin hanyoyin jigilar mai na haramtacciyar hanya da ake amfani da su wajen daukar nauyin kungiyoyin ‘yan ta’adda na kasashen waje.