Qalibaf Ya Jaddaba Bukatar Warware Matsalolin Kasar Iran Ta Hanyar Binciken Ilmi

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf, ya bayyana cewa magance matsalolin da kasar Iran ta ke fuskanta a bangarori da dama zasu warwaru ne ta hanyar masana masu bincike a fannonin ilmi daban-daban. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Qalibaf yana fadar haka ne a lokacinda yake jawabi a gaban […]

Wata Kotun Faransa Ta Daure Jagoran Yan Tawayen Congo A Gidan Yari Na Shekaru 30

Wata kotu a Faransa ta yanke wa wani tsohon jagoran yan tawaye a Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo, Roger Lumbala hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari bayan samun sa da hannu a laifin cin zarafin ɗan adam a yayin yaƙin Congo na biyu, hukuncin da ƴan gwagwarmaya suka bayyana  a matsayin mai matuƙar mahimmanci. An tuhumi Lumbala […]

Sojojin Isra’ila Sun Harbe Wani Matashi Dan Shekaru 17 A Yammacin Kogin Jodan

Sojojin Isra’ila sun kashe wani matashi bafalasdine a ci gaba da kai hare-hare da suke yi a kudancin gabar yammacin kogin Jodan , kamar yadda majiyar lafiya ta yankin falasdinu ta bayyana, Majalisar labarai ta falasdinawa sun bada rahoton cewa sojojin sun harbe matashi ne a kirji a lokacin da suke fito na fito tsakaninsu […]

Iran Ta Bukaci Abi Sahihiyar Hanya Wajen Zaben Sabon Sakatare Janar Din M D D

Rahotanni sun bayyana cewa iran tayi kira da abi sahihiyar hanya wajen zaben sabon sakatare janar din majalisar dinkin duniya , tayi gargadin cewa duk wanda yayi gum da bakinsa kan harin da akai wa cibiyoyin nukiliyar iran hari to bai cancanta ba, a wani jurwaye mai kamar wanka ga shugaban hukumar kula da makamashin […]

Iran da Belarus Sun cimma Yarjejeniyoyi Don Kawar da Takunkuman kasashen Yamma

Iran da Belarus sun sanya hannu kan mahimman yarjejeniyoyi guda uku da nufin karfafa hadin gwiwa tsakaninsu da kuma karya tasirin takunkuman kasashen Yamma akan kasashen nasu. An cimma wannan ne a yayin ziyarar Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi a birnin Minsk yayin ganawa da takwaransa na Belarus, Maxim Ryzhenkov. Jami’an biyu sun sake […]

Grossi: Rasha za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen warware batun nukiliyar Iran

Shugaban Hukumar kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ya bayyana cewa Rasha za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa wajen warware batun nukiliyar Iran. Rafael Grossi ya yi wannan tsokaci ne ga kamfanin dilancin labaran Rasha na Sputnik inda ya bayyana cewa gwamnatin Moscow za ta iya taka mahimmiyar rawa wajen samar da […]

Najeriya: Hauhawar farashin kaya na faduwa a wata na takwas a jere

Bayanan hukuma da aka fitar a ranar Litinin sun nuna cewa hauhawar farashin kaya a Najeriya ta fadi a wata na takwas a jere a watan Nuwamba, wanda hakan ya taimaka wajen raguwar hauhawar farashin kayan abinci. Hauhawar farashin kaya ya kai kashi 14.45% a watan da ya gabata, inda ya ragu daga kashi 16.05% […]

Lavrov: Kasashen Yamma sun mayar da Hukumar IAEA dandalin siyasa

Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov, a wata hira da gdan talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB) a ranar 15 ga Disamba, ya yi magana kan wasu muhimman batutuwa na kasa da kasa, ciki har da shirin nukiliyar farar hula na Iran, yakin Ukraine, da raguwar tasirin kasashen Yamma a duniya. Da yake magana […]